HON SENATOR AHMAD BABBA OF KATSINA NORTH

LightBlog

Breaking

Monday 3 May 2021

HUDUBA ZUWA GA MAGOYA BAYA DAGA SANATA AHMAD BABBA KAITA

 Ga hudubar nan kamar yadda sanata Ahmad Babba Kaita ya rubuta a shafinshi na kafar Facebook:


Bai kamata domin daya daga cikinmu ya kawo wani abun cigaba ga al’umma ba wanan din yazamo abin shagube gugar zana ko cin mutunci ga sauran abokan aikin mu ba.


Mafi yawa daga cikinmu muna bakin kokarinmu kuma ga mai hankali daga yatsun hannuwan mu kadai ya kamata muyi ishara cewa Allah bai raba dai dai ba.


Bugu da kari aikin majalisa kamar sauran ayyukan rayuwane ana koyo ne a hankali a hankali har a qware, saboda haka kuskure ne ka hada sabon zuwa majalisa da tsoho wanda ya gogu babu kamar in akwai masaniyar irin siyasa tadiya darga dake a cikin zauren majalisa.


Saboda haka akasarin ayyuka sun dangata ne largely kan wadan nan factors din.


1)contacts dinka inn n out of the Assembly.


2)Comitees da kake a ciki.


3)kai wane Comittee kake riqe dashi kada mu manta cewa su kansu Comittee’s din grade grade ne akwai A,B,C& D. 


Har wayau ba kowa zai samu Comitee ba biyu-biyu ne a jiha highest kuma ma in an baka Comiteen Tohh wane iri aka baka? 

Wadan nan sune abubuwan la’akari.


Sanin kowa ne tun 2011 nike posting ra’ayina ayyukana recruitments dina da makamantan su don kokarin kamanta adalci ga mazabuna da nike wakilta don saboda in kaucewa hadarin siyasar wariya da nuna son kai, postings dina basuda wata alaqa da wani ko kuma gasa da wani hasali ma duk wanda ya nemi intervention dina a mazabarshi Ina kai mashi dauki shiyasa ayyukana suke fita daga constituency dina. 


Allah yasa mu hankalta.

No comments:

Post a Comment