HON SENATOR AHMAD BABBA OF KATSINA NORTH

LightBlog

Breaking

Tuesday 28 June 2022

AHMAD BABBA KAITA: A CIKIN SHEKARA DAYA



By:  Zahraddeen L. Kafinsoli


Daga farkon shekarar da ta wuce zuwa yau (13 January, 2021 - 09 May, 2022), Maigirma Sanata Ahmad Babba Kaita​​, ya samar da guraben aikinyi a matakin Gwamnatin Tarayya guda Chasa'in da Daya (91) ga Matasa 'yan asalin shiyyar Daura dama Katsina baki daya.


Bayan haka kuma, Sanata Kaita ya rabama Mata da Matasa guda Dari Hudu da Saba'in da Bakwai (477) kayan Sana'oi kala-kala tare da basu horo na musamman da kuma jari domin su dogara da kansu (Masha Allah) duk a cikin shekara daya!


Bugu da kari Sanatan da yake wakiltar Shiyyar Daura a zauren Majalissar Dattawan Nigeria, ya gina azuzuwan karatu na zamani guda Dari da Tamanin da Hudu (184) duk dai a cikin shekara daya, bayan gina asibitoci, gadoji, hanyoyi, famfunan ruwan sha, kasuwa, dakunan kwana na dalibai, da dai sauran su.


Kai, madalla da wakilci irin na Sardaunan Kankia Amadu. Muna rokon Allah Ya cigaba da baka dama da ikon kawo linkin irin wadannan aiyyukan alkairi a cikin al'umma (Amin).


(Yana da kyau mai karatu ya sani cewa, abunda bincikena ya iya tabbatarwa kenan)

No comments:

Post a Comment