
Fita ta 1
A gaskiya mutanan Kankia kusada ingawa, da dama suna jin
dadin wannan Mulkin na Shugaba mai adalci wato Ahmad babba kaita
Musamman Idan akayi al’akari da irin
yadda Gwamnatinsa take ta kokarin ganin ta daqilar da zaman banza da kashe wando a gefen titi, take kokarin ganin dukkan yankuna sun amfana da mulkin sa.
musamman a Yankin ingawa, duba da yadda yazama house to house alherinsa ya game ko Ina.
Mutanan Kankia kusada ingawa, sun shiga cikin wani Hali na rashin
aikin yi da Rashin Kudi, sanadiyar
lalacewar tattalin arzikin constiuency din da suke ciki a sakamakon Shugabancin kama karya gami da handama da baba kere da shuwagabbin da suka gabata suka wanzar acikin wadannan garuruwa.
Kwatsam a Rana tsaka sai gashi Allah ya kawo Wanda ya kawar da waccen dadadden murdadden sankai da aka Dade ana kokowa dashi, amma cikin dakiku kadan yaxama tarihi.
Duba da yadda ya rungumi matasa yai masu Gata acikin gatan Allah mai gata ga kowa, ya maida su mutane a siyasan ce ake damawa dasu har da shawara sabanin da, da saidai suji a makwafta.
Ya Rika kama masu hannu ana samar masu aikin yi domin su dogara da kansu cikin dogaro ga Allah.
Sai kaga mutum yana ci wasuma naci a kalkashin su wato wannan karin maganar na hausawa Abk ya karya Mata kashin baya wato (kowarci shi kadai shi kadai zai mutum) to maganar hausawa ce Dai tunda ba gaskiya bane, amma duk da haka sai yace kowa ya samu to yanemi Dan uwan sa musamman na gidan Abk.
Wasu kuma aka basu wani abin domin suyi sana'o'i wasu aka basu mashin sunemi abinci, duk Dai gasu Nan anata amfana gaba daya.
Yanzu Wanda ke wannan shine mai aibu?, shine abin zagi? Shine abin kushe da hassada??
Shin Wanda ya aikata wannan shine mai adalci ko kuwa wadanda suka gabata?? Ina adalci ga Wanda ya aibata mai wancen aikin????
Mu hade a part 2 domin cigaba da bayyana alherin Wanda ya kyautata.
Bilyaminu Abdullahi majazubi Ingawa

No comments:
Post a Comment