Wannan kafar sadarwar ta Katsina Daily Post News ce ta zabo shi a cikin sauran sanatocin jihar Katsina guda uku bisa cancantarsa.
Mun ba shi lambar yabo ne a matsayin gwarzon Sanatan da ya fi kowane Sanata aiki cikin sanatocin jihar Katsina da muke da su a majalissar Dattawan Nijeriya.
Kadan daga cikin daliban da ya sa muka zabe shi;
Ya kawo makarantar horas da ma'aikatan kashe gobara (Federal Fire Service Training School) a karamar hukumarsa ta Kankiya, kuma tuni gwamna Masari ya bayar da hekta goma domin ci gaba da ginin makarantar.
Ya dauki ko samar wa matasa da dama aikin yi a gwamnatin tarayya, a kuma ma'aikatu daban-daban duk a cikin shekarar ta 2019.
Ya yi fice a cikin sauran sanatocin da muke da su guda uku, wajen ziyartar mazabar da yake wakilta ta shiyar Daura akai-akai.
Yana daya daga cikin yan majalissar Tarayya na jihar Katsina dake sauraren koken al'ummar da yake wakilta.
Yana kuma kokari wajen tashi a zauren majalissar domin gabatar da korafi ko koken abin da shiyar da yake wakilta take bukata daga gwamnatin tarayya.
A takaice dai mun yi amfani da matakai uku wajen fitar da sakamakon gasar kamar haka;
1 Gina Al'umma
2 Gina Kasa
3 Kare Muradun al'ummar da yake wakilta
Kuma duk ya yi su a cikin shekarar 2019
Zuwa anjima za mu kawo maku wanda ya zashe kyautar gwarzon dan majalissar wakilai cikin yan jihar Katsina,
Mun kuma yi wannan zaben ne ba don son ra'ayi ba ko siyasa, mun yi shi ne ta la'akari da abin dake zahiri daidai da kuma fahimtar mu.
Thursday, 2 January 2020
Da Dumi-duminsa: Sen. Babba Kaita ya lashe kyautar lambar yabo ta gwarzon Sanata na 2019
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment