Daga bakin Hon Ahmad Babba Kaita
Gobe ne inn shaa Allah zamu wuce Daura wurin sadakar ukkun marigayi sen madawaki da fatan wanda bai samu hali ba zai saka senator madawaki addu’ar samun rahamar ubangiji jallah jalal sarkin da baya kuskure.
Gashi kuma gobe jumma’atu babbar rana.
Allah ya jiqan madawakin daura ya gafarta kurakurensa na azijancin dan adam ya cika masa ma’auninsa na ayyukan alkhairi da yayi.
Allah yayi masa rahama yasa kwanciya hutu ce.
Ina mana ta’aziyyar wanan babban rashi gaba daya.
Idan tamu tazo Allah ya kyautata karshen mu yayi mana gafara baki daya albarkar fiyayyen halitta.
Wanan kadai ya ishemu ishara da wa’azi kan mu bi duniya a sannu mu kuma zama cikin shiri a koda yaushe.
Allah ya jiqan iyayenmu da ‘yan uwanmu da malaman mu baki daya.
Mu kwana lafiya yanzun na iso kankiya.
Ina kuma cigaba da neman afuwar masoya kan rishin ganina ko tankawa a cikin group Allah ya sani bani zaune ga al’amurra bisa kaina wanda shi Allahn kadai yasan yawansu.
Ina kuma kara neman yafiya saboda rigimar yadda zan amsa massages bata yiwuwa ne kurrum saboda hannuwa biyu kamar kowa kuma massages keep comin kamar ruwan sama ga groups kala kala ga kuma masoya ba’a cewa komi banda Facebook da other social groupings.
Ta kai ga har wadansu suna hassala duk da haka Ina bada hakuri saboda babu yadda zani ga kuma dumbin ayyukan Al’umma wuyana to cikin biyu sai dai inyi daya ko dai inbi ayyukan da zasu taimaka ma al’umar mu ko kuma inyi aikin amsa waya responding to Facebook or engaging in WhatsApp.
Don Allah ina neman afuwarku da kuma fahimtar ku.
Allah ya shige mana a gaba.
Nagode.
Friday, 6 April 2018
Zuwan Hon Ahmad Babba ta'aziyyar Sen Mustapha Bukar
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment