HON SENATOR AHMAD BABBA OF KATSINA NORTH

LightBlog

Breaking

Wednesday, 14 February 2018

DA MUGUWAR RAWA GWAMMA KIN TASHI, DAGA HON AHMAD

Na gama karbar list na applicants daga kankiya, kusada Ingawa duka namasu sha'awar shiga aikin soja, kuma Nafara bakin kokarina don ganin cikin ikon Allah nasamu nasarar fitar da masu rabo wadanda Allah (saw) yacida. Amma wani sauri ba guduba saboda la'akari da abubuwan dasuka faru a baya kai harma da kwana kwanan nan a inda mu karasa guraben yaranmu sojoji har ukku wadanda harma sun gama samun horon soja da kuma wadansu wadanda basu kaiga ko hakan ba yasa dole inyi wanan hudubar. Kuma ya kamata matasa su natsu su fahimci muhimmancin wanan bayanin domin in har bamu saurari shawara ba zamu kwari kawunan mu da kuma na 'yan uwanmu . A duk lokacin da Allah ya baka dama a cikin daruruwan masu nema saika salwantar da ita bisaga ganganci toh ba kanka kadai ka cutar ba ka cutar da wani matashin wanda ta dalilinka samunka kane shi yarasa. Alal misali yaran da aka kora bayan sungama samun horo saboda ganganci wanda za'a iya kauchemawa tun farko yasa sunrasa gurbin kuma sun hana wasu wadanda tun farko sun cancanta susamu, wanda wanan ya saba ma sunna. DON KAUCHEWA WANAN BABBAN KUSKUREN YARA SU KULA DA WADAN NAN SHARUDDAN. 1) Kada kayarda ka bada jarabawar wani domin kana zuwa za'a tambayeka BVN number dinka kuma da an karba za'a gane wanda ya zauna jarabawar haka kuma in ka boye shekarunka za'a gane ta BVN. 2) Medical abinda mostly yake kada yaran mu shine ciwon hepatitis, wanda ya zama ruwan dare a arewacin nigeria kuma mafi yawan al'umma basusan maa suna dashi ba a cikin jikkunansu, kuma abun takaicin duk da kusan kowane asibiti ana iya gane ciwon hepatitis hakan bai samuba. saboda samun nasarar screening da zakuyi kwanan nan ya zama wajibi kowa yaje ayi masa screening tunda cikin ikon Allah duk da hadarin hepatitis yanada magani kuma ana warkewa tangaram cikin qanqanen lokaci. Ni Kaina an taba diagnosing dina da hepatitis kuma cikin ikon Allah nasha magungunna na warke (😭kuma itace sanadiyyar rashin dan uwana Bashir Babba). Wanan gargadin ya zamo wajibi domin hukumar gidan soja ta fada mana a majalisa cewa wancan karon duk yaran dasuka kama da anfani da takardun bogi sun kyale su, bayan sun koresu. tohh amma sun tabbatar mana cewa a wanan karon duk wanda suka kama da anfani da takardun wani sai yaje gidan maza (kunga wanan ba karamin tashin hankali bane.) Ina son in tabbatar maku duk wanda yayi applying inn shaa yanada cikkakar damar samu inn shaa Allah madamar ya cika wadan nan sharuddan. ALLAH YASA MU DACE. SHEKARUN QUALIFICATION 18-25.

1 comment: