Ita dai kyauta ga Hon Ahmad Babba Kaita kusan ince wani al'amari ne wanda basu lissafuwa duk ta yadda mutum zai qidaya saidai mutum yayi iyakar yinshi.
Mai gida Hon Ahmad ya bada kyautar jerseys da Naira dubu dari biyar(N500,000) ga yan wasanmu na Kankia da suka ci kofin shugaban kasa wanda aka sama suna Buhari Cup sai wadanda sukayi na ukku wadanda su kuma yan Ingawa ne aka basu kyautar Naira dubu dari da hamsin (N150,000). Hakika wadannan yan kwallon kafar na Kankia da Ingawa sunyi godiya kwarai tare da addu'ar Allah ya maimaita masu wannan mulkin, nima nace ameen.
Samarma matasa aiki, taimakon marasa lafiya da kudin magani, samar da tsaftataccen ruwan sha da kawo cigaba domin gudanar da rayuwa mai kyau su ne ababen da wannan bawan Allah yasa a gaba. Allah ya maimaita mana mulkin wannan hazikin shugaba wanda mutanensa suka zamto tunaninsa a koda yaushe mai girma Ahmad Babba.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment