Assalamu Alaikum Jama’ar Jihar Katsina
Kamar yadda nayi gayya zuwa rakiya wajen sabunta karin zama d’an Jam’iya, cikin karimci, yarda da girmamawa,da yawa mutane sun amshi goron gayya sun halarci wannan biki ta yarda har bani da isassun kalamun da zanyi godiya daidai da karimcin.
Alhamdulillah anyi taro cikin nasara an kuma tashi lafiya daidai da tsarin mu na siyasar mutuntawa da kuma ra’ayi sabanin siyasar tilasci, tozarci da musgunawa; tsari da Najeriya ta ginu bisa wanda kuma gwamnati mai ci karkashin mulkin Shugaba Buhari take kokarin kawar da Najeriya bisa. Hakika, abin yabo ne ganin yadda dimbin mutane suka halarci bikin, suka kuma tafiyar da lamurran su bisa kyautatawa da mutuntawa musamman Idan akayi la’akari da kokarin da akayi ya karkashin k’asa na haddasa fitina a wajen taron don ganin a gurbata nasarar da akayi hasashen za’a samu. Ina godiya mai dimbin yawa ga duk wanda ya halarci taron, ya kuma bada gudummuwar samun nasarar abin.
Har kullum Ina k’ara tunasar damu, wanda baida kayan talla shike neman fad’a a kasuwa. Hakan yakamata ya zama baitin farko a kundin kowane d’an siyasa. Kamar yadda muka samu nasarar wannan biki ba tare bin tsari na gidadanci ba, to ya zama hujja a garemu cewa nasarar siyasa ba dole sai anyi gidadanci ba. Har abada zan tsaya kan tsari na gina al’umma ba na rusa ta. Zan tsaya kan tsari na bin doka da oda ba nayi masu karan tsaye ba.
Ina godiya ga duk mutanen garin Kankia wadanda suka tsaida harkokin su na yau da kullum, suka karimta ni aka samu nasarar wannan biki. Haka, Ina godiya ga al’ummar Jihar Katsina baki d’aya da suka zo daga sassa daban-daban na Jihar don su tabbatar da nasarar bikin. Hakika, naga karimci kuma Allah Ya saka da mafificin alkhairi.
Godiya ta musamman ga jami’an tsaro da suka tabbbatar da kare doka da oda cikin mutunci ba tare da musguna ma kowa ba. Ina mika godiya ta musamman ga abokai na wadanda suka taso daga wurare daban-daban don su tabbabtar an samu nasarar taron. Alllah Ya k’ara mana zumunci da son juna.
A karshe Ina mik’a godiya ga dukkan wadanda suka aiko da sak’o na fatan alkhairi ta kafafen sanarwar daban daban don nuna goyon baya da k’auna a gareni. Allah Ya biya da mafificin alkhairi. Ina godiya ga Jami’an Jam’iya da suka tabbatar da nasarar taron.
Ina godiya da kuma fatan Kowa ya koma gida lafiya.
Jazakallah
No comments:
Post a Comment