HON SENATOR AHMAD BABBA OF KATSINA NORTH

LightBlog

Breaking

Thursday, 10 September 2020

RAHOTO NA MUSAMMAN DAGA SHIYYAR DAURA JIHAR KATSINA, KAN AYYUKA DA SANATA MAI WAKILTAR SHIYYAR DAURA YA AIWATAR CIKIN MAZABAR CIKIN SHEKARA BIYU.

 


Kamfanin kafar sadarwar zamani (Social Media) mai suna Mobile Media Crew ya fara zag





ayen shiyyar Daura don kawo rahotanni na musamman kan ayyukan raya kasa da Sanata Mai wakiltar shiyyar Daura Sen. Ahmad Babba Kaita ya aiwatar a cikin shiyyar Daura da yake wakilta.


Cikin shekara biyu da hawan Sanata Ahmed Babba Kaita  wakilcin shiyyar Daura, Sanata Ahmad Babba Kaita ya aiwatar da ayyukan raya kasa guda (128) cikin kananan hukumomi goma sha (12) na shiyyar Daura da yake wakilta.


Mobile Media Crew ta fara da duba ayyukan Sanatan daga karamar hukumar Baure, ayyukan da Sanatan ya aiwatar a cikin  karamar hukumar Baure sun hada da!


Sanata Ahmad Babba Kaita ya Gina Karamar Asibiti  mai suna (Comprehensive Hospital) a turance a garin Dankum dake cikin karamar hukumar ta Baure, don inganta harkar kiwon lafiyar yankin.


Sanata Ahmad Babba Kaita ya gina Rijiyar da famfon  tuka, tuka (Borehole) a Garin Madattan Fulani cikin karamar hukumar ta Baure, don samar da ruwan sha mai tsabta a yankin.


Sanatan, Ya gina Makarantar sakandiren Al'umma ta koyon harshen Larabci cikin garin Baure (COMMUNITY ARABIC SECONDARY SCHOOL BAURE) Karamar Hukumar Baure, don inganta harkar ilmin addini a yankin.


Har ila yau Sanatan Ya sanya fitila mai amfani da hasken rana guda goma (10) a cikin Babbar Asibitin Baure ( Baure General Hospital) don bunkasa bangaren kiwon lafiyar yankin.


Sanatan Ya gina Makarantar Islamiyya mai azuzuwa guda uku (Tahfiz Qur'an) Garin Yanduna duka cikin karamar hukumar Baure. Don habbaka Ilmin  addinin musulunci a yankin.


Sanata Ahmad Babba Kaita Ya gina Makarantar firamare mai dauke da azuzuwa guda uku (3) a garin Unguwar Kaura cikin karamar hukumar ta Baure. Domin inganta harkar ilmi a yankin.


A nashi jawabin lokacin da Mobile Media Crew ta ziyarci Makarantar sakandiren Al'umma ta koyon harshen Larabci dake cikin garin Baure da Sanatan ya gina, shugaban Makarantar Malam Ahmad Muhammad Abbas ya "yabama Sanatan kan yadda yake kokarin sabke nauyin da aka Dora mashi na wakilcin shiyyar Daura. Daga karshen Malam Ahmad Abbas yayi addu'ar fatan alheri ga Sanatan.


Suma Al'ummar Madattan Fulani da suka amfana da Rijiya (Borehole) da famfon tuka, tuka cikin aikace, aikacen Sanatan, sun bayyana godiyar su da fatan alheri ga Sanatan cikin harshen fulatanci, don yankin gaba daya ko hausa basuji duk rugar fulani ce, sun bayyana "cewa kafin su samu wannan Rijiya, ruwan tafki mara kyau suke amfani dashi, wanda ya rika haddasa masu cututtuka dasu da dabbobin su.


Rahoto.

Surajo Yandaki

Editor, Mobile Media Crew

09, September 2020.


Allah yasaka da alkhairi sanata Ahmad Babba Kaita

No comments:

Post a Comment