HON SENATOR AHMAD BABBA OF KATSINA NORTH

LightBlog

Breaking

Tuesday, 11 September 2018

TAIMAKON N100,000 GA WATA MARAR LAFIA DAGA SEN AHMAD

Alhamdulillah! An nema kuma ansamu, Allah ya sharemaka matsalolinka baki daya kaf, kamar yarda kake sharema talakawa nasu amen Sen. Ahmed Babba Kaita. Sako yaje inda akeso; Yanzu haka iyayen wannan yarinya sun amshi cikon kudin da suka nema wajen Sen. Ahmad Babba Kaita Naira Dubu Dari Daya (100, 000: 00). Sen. Ahmed Babba Kaita iyaye da Dangi da makwabta na wannan yarinya na godiya marar adadi akan abunda kaimasu na alkhairee. Allah yasaka maka da mafificin alkhairee ameen. Muna addu'a Allah yasa ayima wannan yarinya aiki lafiya, Allah kuma yabata lafiya mai dorewa ameen. Kai Tsaye Zuwa Ga Sen. Ahmad Babba Kaita: Iyayen wannan yarinyar daga Garin Bindawa Local Government Area, Daura Senatorial Zone, Katsina State. Suna neman taimakonka na kudi domin yima tiyarsu aiki a: Aminu Kano Teaching Hospital Kano. Sudai iyayen wannan yarinyar sun nemi taimakon wajen al'umma kuma ansamu, saidai ba duka ba. Ita dai wannan yarinya za'ayimata aiki a Aminu Kano Teaching Hospital Kano, akan kudi Naira Dubu Dari Biyu (200, 0000: 00), inda yanzu haka Uwar Gidan Gwamnan Jahar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari ta bayar da Naira Dubu Dari Daya (100, 000: 00), yanzu ana Neman sauran Naira Dubu Dari (100, 000: 00) domin cirema wannan yarinyar ruwa akanta, a Aminu Kano Teaching Hospital Kano. Allah ya bata lafiya da sauran yan uwa musulmai ameen. Allah yaba Sen. Ahmed Babba Kaita ikon taimakawa ameen. Sen. Saidai ankara hakuri....... Anwar Nuhu Kankia 7/9/2018 #TeamABK4Senate

No comments:

Post a Comment