Tun bayan da Sanata Engr. Mustapha Bukar (Madawakin Daura) ya rasu, talakawa suka shiga halin kunci tare da jimami akan wannan babban rashi sakamakon ayyukan alkairi da ya shimfida a dukkan kananan hukumomi goma sha biyu (12) da suke karkashin shiyyar Katsina ta gabas. Wasu ayyukan an kammala wasu kuma ana cikin gudanar da su amma Allah bai bada ikon cikawa ba. Akwai ayyukan ruwan sha, gina dakunan karatu a makarantu, samar da hasken wutar lantarki, bada ayyukan yi ga matasa, tallafin Kasuwanci ga mata da matasa tare da sauran wasu muhimman ayyuka da marigayi Madawaki ya aiwatar ga wannan yanki namu. Ba zamu taba mantawa da shi ba kuma a kullum muna yi masa adduar Allah ya kai haske kabarin sa tare da sakayya da gidan aljanna.
A bangaren neman wanda zaya gaje sa, yan siyasa da dama sun nuna sha'awar tsayawa takarar kujerar tare da cigaba da shiga lungu da sako na wannan yanki namu domin neman amincewar masu ruwa da tsaki a harkar tare da neman goyon bayan talakawa domin samun damar wakiltar su a majalisar dattijai. Yan takara akalla goma sha biyu ne suka bayyana ra'ayin su kuma suka sayi tikitin takara a jam'iyya mai mulki yanzu.
Bayan anyi zaben fidda gwani, Hon. Ahmad Babba Kaita shine ya samu nasara da kuru'u 1,723. Wannan nasara ta samu ne a sakamakon ayyukan alherin da yake yi ma yankin sa na Kankia/Kusada/Ingawa wanda sune yake wakilta a majalisar wakilai tun daga shekarar 2011 har zuwa 2018. Ahmad Babba Kaita yayi fice a zauren majalisa a bisa irin gudunmuwar da yake bayar wa wajen kawo kuduri masu kyau domin samun sauki ga talakawan Nijeriya. Baya wasa da damar sa a duk lokacin da ta zo masa. A bisa wadannan dalilan ne "Delegates" suka amince da su zabe sa a matsayin wanda zaya kara da abokan hamayyar sa na jam'iyyun adawa.
Da wannan muke kira ga dukkanin jama'ar wannan yanki namu na Daura da su fito ranar zabe domin su zabi Ahmad Babba don samun damar ci gaba da ayyukan alherin da marigayi Madawaki ya fara.
Wednesday, 8 August 2018
HON AHMAD BABBA NE ZABIN TALAKAWA A DAURA ZONE
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment