JAWABIN AHMAD BABBA KAITA NA YAU ATAKAI CE.
Dakin taro yacika ya batse da dumbin masoya kowa yanata farin ciki Ana gaisawa da juna, Alhamdulillahi, bayan kammaluwar jawabi daga wakilan kananan hukumomi, WATO (Kankia ingawa kusada) Sai mai gayya mai aiki ya rufe da jawabi kamar haka.
AHMAD BABBA KAITA YANA CEWA "assalamu alaikum, bisimillahi sami'ul alim, Ina godiya Ga allah da yahada mu a wannan bagire mai Albarka a Karo na biyu, lallai Ina farin ciki sosai duba da yadda muka hadu Anan saboda soyayya gashi harma wadanda basu cikin kenan hukumomin da nake wakilta, wanda nasan cewa kaf mutanan da suka zo nan sunzo ne saboda nuna soyayya, indan kudi ne wani Nan banda kudin da zan bashi yazo Nan, Dan wanima yafini kudin.
Sannan Ina bada hakuri, domin da yawa Anan dama wadanda basu zo nan ba wasu kila mun masu badai dai ba, saboda halin yau da kullum musamman masu kirana ko text message suga ba reply, hakan yasamu asaline daga yawan masoya Wanda nasan bazan iya maidawa kowa ba Amma ai man afuwa dan nima dan Adam ne kamar kowa.
A fannin Facebook and whatsapp kuwa Shima saidai ban hakuri domin ba sosai nake reply ba, SABODA nima hannu na biyu kamar kowa, Kuma a time daya Sai asamu sako sama da nawa, Ina ba kowa hakuri, Dan yanzu saima inyi sati 3 ban hau online ba saboda hidindimun sunyi yawa saidai wata ran nadan leko agaisa ayi wasa da dariya in fita.
Sannan dukkan wannan abubuwa da muke yi na alkairi kune qashin bayan sa, domin kokarin da kuke a kullum shine ganin anci gaba, Kuma wannan shine yake karfafa mu, Kuma fatan mu shine muci gaba da aikin alkairi dan in mune yau gobe ba mu bane shi kuma alkairi Dan ko ne baya faduwa QASA banza, Kuma wata kila Anan cikin Ku Allah yana iya daukaka wani ya kaishi wannan matsayin Kuma muma masu kama masa ne Dan ganin an kyauta tawa al'ummar yankin mu.
Ahmad babba kaita yayi jawabai masu yawa najan hankali da ratsa zukatan masu saurare, inda akarshe ya yabi shugaba BUHARI ya yabi Yan uwa masu son ci gaba irin shi, kamar Hon. Abubakar Yahaya kusada, inda har yadan bada history din tafiyar siyasa ta Garin kusada a takai ce Wanda time bazai barni na fada ba dan saukaka ma mai karatu".
Alhamdulillahi taro ya tashi lfy anyi ZIYARA kowa yaga kowa fatan mu Allah ya Kara hada mu acikin wannan zumunta, lallai a yau Abk ya nunawa Duniya cewa shi ba raggon shugaba bane kai wani Abu MA Sai Wanda ke wajan, anci ansha aljihu ya dauka Alhamdulillahi, masu fushin wannan suji haushi, Kankia ingawa kusada ta AHMAD BABBA KAITA CE DA IKON ALLAH.
ALLAH YA MAIMAITA MANA HON AHMAD BABBA KAITA
Sunday, 4 March 2018
Jawabin mai girma Hon Ahmad Babba Kaita a wajen taron masoyanshi na 4/3/2018
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment