HON SENATOR AHMAD BABBA OF KATSINA NORTH

LightBlog

Breaking

Sunday, 12 August 2018

GODIYA TA MUSANMAN DAGA HON AHMAD BABBA KAITA

Assalamu alaikum wa rahammatullahi ta'ala wa barakatuhu! Bayan gaisuwa da fatan alkhairi, zanyi amfani da wannan dama in mika godiyata ga daukakin al'ummar Jihar Katsina dan nuna goyon baya da sukayi wajen tallafa ma jam'iyar APC da gwamnatin jihar wajen kare mutunci da martabar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a zaben cike gurbi na d'an majalisar dattawa, wanda aka gudanar jiya, kuma wanda na wakilci jam'iyar mu mai adalci, APC a matsayin d'an takara kuma Allah Ya bamu nasara muka lashe da kyakkyawan rinjaye. Ba karamin abin alfahari bane ganin yadda talakawa suka jajirce wajen ganin an samu nasara a wannan zaben. Wannan na nuni da gamsuwarsu kenan kan irin namijin kokarin da gwamnatocin APC a matakai daban-daban sukeyi wajen sama ma al'umma mafita daga matsatsin da PDP ta jefa Najeriya. Abin jin dadine ganin yadda, duk da karyace karyace, yarfe-yarfe da makircin PDP don ta haddasa rashin yarda tsakanin talaka da shugabanni, har yanzu dai auren amana dake tsakanin talaka da APC na nan daram dam ba ko yaji ballantana saki. Hakika, wannan nasara da muka samu zata kara ma Shugabanninmu karfin guiwa wajen sama ma al'umma mafita. Illa iyaka, yadda kuka toshe kunnawanku kuka ki sauraren farfagandar PDP cewa APC ta gaza, to kuci gaba da amincewa da kyakkyawar niyyar shugabanni APC na tabbatar da chanji mai amfani a Najeriya ta bin hanyoyin da suka dace wadanda suka daidaita da tunani na hankali. Alhamdulillahi, anyi zabe an gama kuma an sami nasara. Kamar yadda abaya kuka turani wakilci a karamin zauren majalisa, naje, kuma na kare mutunci da martabarku, to yanzu ma da kuka kara turani babban zauren majalisar, ba wani abu zance ba illa ince an bugi kura a kai an kara mata karfi. Matsayata shine inyi wakilci na adalci cikin yarda, girmamawa da mutuntawa tsakanina da ku. Ina mai baku tabbacin cewa abinda za'a gani gaba yafi wanda aka gani a baya. Dole in yaba ma Shugaba Buhari kan namijin kokarin da yakeyi don daidaita al'amurran Najeriya. A bisa haka ina baku tabbacin cewa zamana a zauren majalisa dattawa baida banbanci da zamanku cikin zauren majalisar don kare martaba da mutunci Shugaban Buhari. Abin bakin cikine ganin yadda wasu tsirara suka jajirce suna shakiyanci a majalisar don ganin sun kawo cikas ma kokoarin da shugaba Buhari keyi na inganta rayuwa a Najeriya. Ba wani abu yakawo wannan ba illa aga a zabe na gaba an kori Shugaba Buhari an sake maido mulki irin na shirme, sakarci da shagali wanda PDP ta ginu a bisa. Da yardar Allah zamu tsaya muga duk wani d'an kwanta-kwanta, duk kwarewarshi a makirci, sai mun sa mashi takunkumi don sama ma Shugaba Buhari damar cigaba da kokarin inganta rayuwa ma talakawan Najeriya. Ya zama wajibi inyi yabo ga Maigirma Gwamna (Dallatu) Aminu Bello Masari, ganin irin jajircewa da yayi na ganin anyi zabe na adalci cikin zaman lafiya da lumana. Hakika Gwamna ya ciri tuta wajen tsayawa bisa turbar da aka kafa jam'iyar APC, turbar gaskiya da adalci. Allah Ya Kara mashi karfin guiwa wajen sauke nauyin mulki da Allah Ya dora mashi. Ganin yadda al'amura suke daidaita a Jihar Katsina duk da makirce-makirce da karyace-karyace na y'an adawa, hakika Gwamna Masari ya chanchanci yabo. Ina kira ga al'umma da aci gaba da bashi goyon baya don ganin an samu nasarar tafiyar. Daga zaben fidda gwani zuwa babban zabe na jiya, duk mai hankali zaisan cewa shugabanni jam'iyar APC na jihar Katsina tsaye suke kan turba irin ta Mai girma Gwamna, turba ta tsare gaskiya bisa adalci. Sun nuna chanchantarsu kan tafiyar da al'amurran jam'iya. Wannan yasa dole in yaba masu kuma inyi addu'a Allah Ya Kara masu karfin guitar wajen kare martabar APC, Shugaba Buhari da Gwamna Aminu Bello Masari ta hanyar tafiyar da jam'iyar bisa tsari na APC na tabbatar da adalci. A karshe zanyi godiya ga dukkan wanda ya taimaka koda da kyakkyawar kalmar bakine har aka samu wannan nasara. Hakika yanzu kowa ya fahimta cewa an wuto zamanin da ake cusa kan talaka cikin tukunya a dora bisa murhu a dafashi da ranshi. Yanz

No comments:

Post a Comment