Tawagar Mai Girma Sanatan Katsina Ta Arewa - Hon. Ahmad Babba Kaita ta safka Karamar Hukumar Mani domin ayi masu godiya da bangajiya akan kokari da gudunmuwar da suka bayar har aka samu wannan nasara.
Sanata Ahmad yayi godiya kwarai da gaske tare da fatan alkairi. Yayi masu alqawarin gina famfo guda 20 tun kafin ya kama aiki.
Daga karshe ya basu kyautar N500,000 sakamakon kokarin da suka yi a zaben fidda gwani kuma sune suka zama na Biyar wajen yawan kuru'u a zaben da aka gudanar jiya. Sun bada kuru'u 20,479.
#TEAMABK4SENATE
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment